Hassada waka ce da shahararran mawakin hausamp3 wato Nura M inuwa yayi domin jan hankalin mutane adaina hassada domin komai yana wucewa.
Ga kadan daga baitocin mawakin:
Nayi banyi daidaiba Nura m Inuwa ke kira gunku masoya.
Ehhh Ku mu daina hassada tunda kunga komai Yana wucewa Kufa kyale duniya lamarinta tsoro yake sakawa.
Ita Duniya budurwar wawace haka naji zance,
Haka hassada kamar takine ajikin ya'yan itace,
Sannan mu tababbata da na tsaye ya wuce na kwance.
Sara da sassaka gamji ai tamar kasa bashi jewa.
Mufa daina hassada tunda kunga komai
Yana wucewa, Kufa kyale duniya lamarinta tsoro yake sakawa.
Inkun tina akwai rani kafin a iske kaka, 
komai duhu da rana tazo koina ta haska,
Murna tana ga mai noma in damina ta sauka,
kuma dena cusa kai kyau na tafiya saida waiwayawa.
Kufa daina hassada tunda kunga komai
Yana wucewa Kufa kyale duniya lamarinta tsoro yake sakawa.
Dukkan abinda akaje aza sama ba rabo na kwado,
aiki yana ga wanda ya ke debar ruwa da kwando,
Yan yara yara su akaima barazana da dodo,
zomo akan gudu dole a kyaleshi yai wucewa.
....Har zuwa Karshen Wakar.
Sauke wakar DOWNLOAD

Post a Comment

Write your comments here

Previous Post Next Post