mina Muhammad (Amal) ‘yar asalin Æ™asar Kamaru ce, wadda a yanzu ta fara haskawa a finafinan Kannywood. Jaruma ce da a yanzu ta fara shahara sakamakon manyan finafinan da take fitowa a cikinsu. Musamman da take taka rawa tare da shahararrun jarumai irinsu: Ali Nuhu da Adam A. Zango. A wannan ‘yar gajeriyar tattaunar da ta yi da Mubarak Umar, ta É—an taÉ“o batun faÉ—in tashin da ta yi kafin ta zo Nijeriya, har ma ta fara fim É—in Hausa.
Ki gabatar wa da makaranta kanki…
Sunana Amina Muhammadu, daga ƙasar Kamaru na zo Nijeriya. Na yi karatuna tun daga furame har sakandire a Kamaru, duk cikin harshen Faransanci. Daga bisani na halarci wata tsangaya da ake koyar da Turanci a can Kamarun, na koya cikin wata uku. Yanzu ina jin yare huɗu, Fulfulde, Hausa, Faransanci da kuma Turanci. Wannan shi dai a taƙaice.
Ta yaya aka yi kika zo Nijeriya?
To, a lokacin da nake Kamaru ina kallon finafinan Hausa, kuma ina jin daÉ—in yadda ake nuna al’adar Hausa. Na koyi abubuwa da yawa dalilin fim É—in Hausa, tun daga kan sanya sutura irin su; atamfa, abaya, leshi da sauran su. Haka zalika, salon maganganun da ake amfani da su, suna matuÆ™ar birge ni. Don nakan kwaikwayi abubuwa da dama.

Post a Comment

Write your comments here

Previous Post Next Post